ACCRA, GHANA - Kudirin wanda aka yi wa kwaskwarima, bayan kotun kolin kasar ta dakatar da fara aiwatar da dokar da farko, inda tace sashe na 43 na dokar ya ci karo da sashe na 106 na kundin tsarin mulkin kasar, a halin yanzu ya baiwa ma’aikatar harkokin cikin gida ikon ba da lasisin noman tabar wiwi ga wadanda suka dace bayan shugaban kasa ya rattaba hannu a kai.
Kakakin Majalisar dokoki, Rt. Hon. Alban Bagbin ya ce, bayan karatun dokar miyagun kwayoyin ta 2023, karo na uku, dukan 'yan Majalisar sun amince da dokar babu ko daya da yace a’a.
Nana Kweku Agyeman, shugaban kungiyar Hempire na Ghana, kungiyar dake fafutukar tabbatar da wannan doka, ya yi bayanin banbancin tabar wiwi da aka zartar da dokar nomawa a Ghana da kuma irin tabar wiwi da ake sha domin nishadi ko maye. Ya ce “tabar wiwi na masana'antu na girma zuwa tsayin kusan kafa 15, kuma ganyen siriri ne jikin reshe mai kauri kuma yana kunshe da sinadarin THC na 0.3 cikin 100; amma tabar wiwi na nishaɗi ko maye na tsayin kimanin kafa 7, kuma ganyen na da faɗi da wasu kwayoyi.”
Har yanzu dokar hani da shan tabar wiwi don maye da nishadi na nan, kuma duk wanda aka kama zai fuskanci hukuma, kamar yadda, Dr. Salisu Ango, likitan kwakwalwa da ilmin halayyar dan Adam ya yi kira ga matasa da kada su yi wa wannan doka rashin fahimta.
Wasu al’ummar Ghana sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi game da zartar da wannan kudurin da Majalisar dokokin ta yi.
Kasashen da suka zartar da dokar halatta noman tabar wiwi domin kiwon lafiya, kimiya da masana’antu sun hada da Zimbabwe, Afirka ta Kudu, Uganda, Malawi, Zambia, Rwanda, Uruguay, Kanada, da Thailand.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah:
Dandalin Mu Tattauna