Shelkwatar rundunar sojojin saman Najeriya, tace jiragen ta sun kai farmaki tare da rugurguza daya daga cikin manyan sansanonin mayakan 'yan ta'adda na ISWAP a yankin tafkin Chadi.
Mai magana da yawun shelkwatar ya shaidawa VOAHausa cewar, wani gaggarumin hari da suka kai ta sama, inda suka dinga luguden wuta akan 'yan ta'addan a sirin yankin Chadi yayi nasara.
Shugaban ya kara da cewa jiragen su masu leken asiri suka tattaro masu mahimman bayanai, nan take suka dauki jiragen yakin su na Alfa Jet suka kai hari kan 'yan ta'addan.
Ya kuma cewa sabo da wannan hari da suka kai, sun rugurguza kayan amfanin 'yan ta'addan da kuma na'urar su ta wutan lantarki da sauran kayan amfanin su.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5