Sojojin Ruwan Najeriya Sun Gano Wasu Haramtattun Matatun Mai

Hoton mai kwance kan ruwa a yankin Ogoni na NIger delta a kudancin Najeriya, kusa da wata matatar mai ta 'yan fasa kwabri, 24 Maris 2011

Rundunar sojojin ruwan Najeriya ta rugurguza wasu haramtattun matatun Mai na tsagerun Niger Delta.

Hedkewatar sojojin ruwa ta Najeriya, tace dakarunta sun sami nasarar gano haramtattun matatun mai a jihohin Delta da Rivers. Daraktan watsa labaru na rundunar sojan ruwa kwamanda Christian Odogwu Ezekobe ya yiwa wakilin sashen Hausa karin bayani.

Inda yace “ A yan kwanakin nan mun sami nasarar rugurguza matatun Mai guda biyar da tsagerun Niger Delta suka yi, uku a Warri, biyu kuma Port Harcourt.”

A cewar Ezekobe, duk inda sojojin suka sami haramtattun matatun mai sukan rugurguzasu ba tare da bata lokaci ba, suna yin hakan ne domin guraren na lungun sarkakiyar yankin Niger Delta ne, kuma yana da hawala a kwaso na’urorin da suke amfani da su wajen tace Man.

Tsohon ministan Fetur a Najeriya, Alhaji Umaru Dembo, yace ire iren wadannan haramtattun matatun Mai na samun Man ne ta hanyar fasa bututu, inda suke hana ruwa gudu ga sauran halattattun matatun Mai. Haka kuma sukan sayar da Man da suka tace cikin arha domin kyansa bai kai yadda ya kamata ba.

Saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Ruwan Najeriya Sun Gano Wasu Haramtattun Matatun Mai - 2'05"