Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Yace Zai Aiki da Hukumcin Kotun Kasa da Kasa A Kan Iyaka da Kamaru


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari yace gwamnatinsa zata yi aiki da hukumcin kotun kasa da kasa da ta yanke akan kasar da Kamaru

Shugaban na Najeriya ya bada tabbacin ne yayinda yake karbar bakuncin jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman Mohammad Ibn Chambas.

Shugaban ya kara da cewa gwamnatinsa ba zata hana ruwa gudu ba a harkokin ayyukan kwamitocin majalisar kan shata iyaka da Kamaru.

" Zamu yi aiki da shari'a.Tunda muka amince da hukumcin na kotun kasa da kasa a shirye muke mu yi aiki da shirin tsaro da tsare tsare tsakanin Kamaru da Najeriya domin a fitar da iyaka", inji Shugaba Buhari.

Shugaba Buhari ya tabbatar da cikakken goyon bayansa tare da tunawa da lokacin da yake shugaban kasa a shekarun 1984 zuwa 1985 lokacin da gwamnatinsa ta kaddamar da shata iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin zuwa yankin Bakassi. Saboda haka yayi gargadin a bar kwamitocin su yi aikinsu kamar yadda hukumcin kotun ya tanada.

Tun farko Mohammad Ibn Chambas wanda ya jagoranci kwamitin din Majalisar Dinkin Duniya ya shaidawa Shugaba Buhari cewa sun kammala aiki akan iyaka mai tsawon kilomita dubu biyu da daya cikin dubu biyu da dari daya da suka taba kasar da Kamaru. Saura tsawon kilimita casa'in da tara su kammala.

Muhammad Ibn Chambas ya yi amannar za'a kammala sauran aikin cikin watanni uku na farko a shekara mai zuwa saboda zaman lafiya da aka samu bayan an kakkabe 'yan Boko Haram da suka mamaye yankin da can.

XS
SM
MD
LG