Sojojin Pakistan sun fada yau Talata cewa sun bude wuta ne biyo bayan sabawa wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta ne da aka karya, abinda yasa sassan biyu suka budewa juna wuta.
Sai dai India tace sojojin na atisaye ne kwatsam sai suka ji sojojin na Pakistan sun dirar musu. Sakamakon wannan musayar wutar ba a samu sojan kasar India ko guda da ya mutu ba, amma a ranar asabar din data gabata sojojin India guda hudu aka kashe a Pakistan sakamakon tsallake wani layin da suka ce ya raba tsakaninsu.
Haka kuma a ranar Litinin din sojojin Indiyan sun kashe wani Noor Mohammed Tantray, shugaban ‘yan gwagwarmayar sa kai mai suna Jaish-e-Mohammed a garin Srinagar da ke kusa da birnin Kashmir.
Wanda ya mutu sakamakon wani fada da ya barke tsakanin ‘yan kungiyar da ‘yan sanda a wajen birnin wannan gari, kamar yadda ‘yan sandan suka bayyana.