Sojojin Najeriya Sun Mamaye Kamfanin Jaridar Daily Trust

Sojojin Najeriya

Sojoji dauke da manyan makamai sun rufe ofishin yanki da Hedkwatar kanfanin Jaridar Daily Trust a Biranen Maiduguri da Abuja, kan labarin kwace garin Baga da Jaridar ta ce mayakan Boko Haram sun yi.

Mataimakin babban Editan Jaridar Daily Trust, Mallam Mahmoud Jega, ya shaidawa Sashen Hausa cewa, sojojin sun isa wurin suna neman wani dan jaridar kamfanin mai suna Hamza Idriss, amma basu sameshi ba, sai suka umarci duk ma'aikatan dake bakin aiki su bar wurin ba tare da bata lokaci ba, Su ka garkame kamfanin bayan sun kashe baki daya na"urorin kamfanin.

Mahmud ya ce, can ma a ofishin kamfanin dake Arewa maso gabashin Najeriya sojojin sun je suna neman Hamza Idriss, amma da basu sameshi ba suka cafke wasu ‘yan jaridun kamfanin guda biyu.

Mataimakin babban editan yakara da cewa, hakan baya rasa nasaba da labarin da Jaridar ta buga cewa, mayakan Boko Haram sun fatattaki sojojin daga garin Baga, sannan ta kara buga labarin cewa sojojin na tattaruwa domin sake kwato garin na baga.

Tuni dai kungiyar ‘yan jaridun Najeriya ta yi Allah wadai da wannan mataki na sojojin tana mai bayyana cewa barazana ne ga dimokradiyya.

Amma mai magana da fadar shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu, ya fitar da wata sanarwa wadda ta umarci sojojin dasu janye daga kamfanin jaridar ta Daily trust.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina

Your browser doesn’t support HTML5

Niajeriya: Sojoji Sun Rufe Kamfanin Jaridar Daily Trust