Mataimakin Daraktan cibiyar tattara bayanai kan dauki ba dadin da dakarun kasar ke yi a hedkwatar tsaron kasar, Brigediya Janaral Abdullahi Haruna Ibrahim ke bayyana haka yayin da yake jawabi a taron manema labaru.
Janaral Ibrahim ya ce anyi wannan kwanton bauna ne biyo bayan wani rahoton sirri da mayakan suka samu. wanda ya kai ga cafke wasu masu hada kai da yan ta'addan.
A wani harin kwanton baunan na daban, dakarun sun sami nasarar hallaka wani babban kwamandan mayakan na Boko haram, a kan dutsen Mandara da ke yankin karamar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Sojojin rundunar Operation Hadin kai sun kuma sheke yan ta'addar Boko Haram 24, su ka cafke guda goma a raye, kana aka kubutar da wasu mutane 35 da yan ta'addan ke garkuwa da su.
Bugudakari, su ma jiragen yakin sojin saman Najeriya na can na ta barin wuta a sansanoni daban daban na yan ta'addar da rahotanni ke nuna ana samun nasara sosai.
A cewar Abba Aji Elder da ke zama daya daga cikin kwamandojin da su ka assasa kungiyar civilian JTF, tun farko anyi sakacin barin wannan fitina ba a mata tufka ba, ta yadda tai ta ruruwa sannu a hankali da yanzu ta ke kusan shekaru goma sha hudu.
Amma duk da haka, a iya cewa ana samun nasara musamman in an duba daga inda aka fito da kuma halin da ake ciki yanzu.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5