Ministan tsaron Najeriya, Birgediya Janal Mansur Dan Ali, yace an kwashe kimanin watanni shida zuwa bakwai ana shirin shiga dajin, sai bayan da ruwa ya ‘dauke aka samu gano ainahin inda ‘yan Boko Haram din suke, sojojin sama sun jefa bama bamai kafin sojojin ‘kasa su shiga su tarwatsasu.
Duk da cewar an fatattaki mayakan Boko Haram daga sansanin karshe da ya rage a hannunsu, an kuma samu ceto mutane masu yawan gaske, kasancear an dade ana bayyana cewa ‘yan matan Chibok na cikin dajin gashi kuma an sami wannan nasara ko ina ‘yan matan suka shiga ne? A cewar ministan tsaro wadanda aka samu an fito da su, kuma yawancin matan sunyi aure sun hayyafa wanda yanzu haka ba lalle bane ace za a iya banbantasu ba.
‘Yan kungiyar kwato ‘yan matan Chibok na bukatar sake lalubawa domin gano dukkan matan da ake neman, wadanda har yanzu suna kan bakarsu na ganin gwamnati ta cika alkawarin da tayi na cewa zata bukutar da ‘yan matan baki ‘dayansu.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5