Sojojin Najeriya Sun Ceto Mutane Sama Da 1600 Daga Hannun Boko Haram

Wasu Daga Cikin Mutanen Da Sojoji Suka Kubutar Daga Hannun 'Yan Boko Haram

Hedikwatar Sojin Najeriya ta ce dakarun kasar sun yi dirar mikiya a wata maboyar mayakan Boko Haram, inda suka hallaka ‘yan Boko Haram 21 kuma aka ceto sama da mutane 1600.

Kakakin sojin Najeriya Birgediya Janal Sani Usman Kuka Sheka, ya ce birged ta 22 dake karkashin runduna ta bakwai sun kai farmaki wasu kauyuka 10 dake karkashin karamar hukumar Kala-Balge a jihar Borno.

An kuma fafata tsakanin dakarun Najeriya da ‘yan Boko Haram din dake boye a kauyukan, wanda yayi sanadiyar kashe ‘yan Boko Haram 21 aka kuma samu makamai.

A cewar Kuka Sheka, ‘daya daga cikin kauyukan akwai wani gari da ake kira Gyarawa inda akwai mutane 1,223 wadanda ‘yan Boko Haram ke rike da su, sojojin Najeriya sun sami nasarar kwato su daga hannun ‘yan ta’addar, an kuma kaisu sansanin ‘yan gudun hijira na garin Rann.

Duk da gumurzun da sojojin Najeriya suka yi da ‘yan Boko Haram, babu wani sojin Najeriya da ya samu rauni a fafatawar. Haka kuma duk inda sojojin Najeriya suka sami labarin akwai ‘yan Boko Haram a wani waje suna kai hari.

Domin Karin bayani ga tattaunawar Hassan Maina Kaina da Kakakin sojin Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Najeriya Sun Ceto Mutane Sama Da 1600 Daga Hannun Boko Haram - 2'13"