Honorabul Abdulhadi Abdullahi Kankara, tsohon shugaban karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, ya koka dangane da matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa a jihar ya kuma yi kira ga mahukunta da su kara zage damtse don ganin an gano bakin zaren.
Amma shelkwatar sojojin Najeriya ta ce ta na kara jan damara don wanzar da zaman lafiya mai dorewa a jihar. A ta bakin Kanar Aminu Ilyasu, jami'in sadarwa na sashen aikace-aikace a rundunar sojin ya ce a yayin da ake kaddamar da shirin Operation Sahel Sanity, sun tsananta kai farmaki akan ‘yan bindigar ta hanyar kakkabesu da fatattakarsu daga maboyarsu.
Ya kara da cewa sojojin su na kuma yin kwanton bauna kan miyagun tare da cafke wasu masu basu bayanai da hakan ya kai ga cimma nasarori da yawa, ciki har da hallaka wasu daga cikin manya-manyan ‘yan bindigar tare da kwato makamai da kuma kubutar da wadansu da aka yi garkuwa da su.
Kwamred Kabir Shehu 'Yan Daki, shugaban wata kungiya da ke tattara bayanai kan rikice-rikice a jihar Katsina, ya ce babu shakka sojojin na iya kokarinsu sai dai hakan bai hana 'yan ta'addar yin kazar-kazar ba.
Saurari cikakken rohoton Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5