Sojojin Najeriya Sun Sha Alwashin Mayar Da Martani Kan Kungiyar IPOB Bayan Ta Kashe Dakarun Soji Biyar

'Yan Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra, IPOB

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana a ranar Juma’a cewa ‘yan aware a yankin kudu maso gabas sun kashe sojoji biyar a wani hari da suka kai a wani shingen binciken ababan hawa.

Kungiyar na masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) dai ta musanta hannu a harin da aka kai ranar Alhamis, a daidai lokacin da yankin ke bikin tunawa da mutane sama da miliyan daya da suka mutu a yakin Biafra da kuma yunwa, rabin karni da ya gabata.

Rundunar ta zargi bangaren kungiyar ta (IPOB) masu dauke da makamai, inda ta ce ta kai wani harin ba zata ba tsammani a shingen binciken ababan hawa da ke kusa da birnin Aba na jihar Abia.

“Abin takaici ne yadda ‘yan ta’addar kungiyar ‘yan awaren IPOB da ESN suka afkawa dakarunmu tare da hallaka wasu a shingen binciken ababen hawan dake mahadar Obikabia cikin karamar hukumar Obingwa ta jihar Abia, daura da garin aba”.

“Don haka, ya zama wajibi rundunarmu ta dauki fansa akan wannan mummunan harin da aka kaiwa dakarunta. martanin rundunar ba zai zama mai kyau ba. Zamu tabbatar da tsattsaran matsin lambar soji akan kungiyar domin ganin bayanta gaba daya”.

“Harin ya yi sanadin mutuwar mutane biyar,” in ji Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba a wata sanarwa da ya fitar.

Sojojin Najeriya

Kungiyar IPOB wacce ke son a kafa wata kasa ta daban ga kabilar Igbo a kudu maso gabashin Najeriya a kullum ta musanta cewa ita ce ke kai hare-hare, wanda a cewarsu, kungiyoyin masu aikata laifuka da 'yan adawar siyasa ne ke amfani da sunan kungiyar.

"Mun yi Allah wadai da harin da aka kai kan sojoji da ke bakin aiki a Aba," in ji mai magana da yawun kungiyar, Emma Powerful, inda ya zargi "masu aikata laifuka".

Batun ballewa dai wani batu ne mai matukar muhimmanci a Najeriya, inda yakin basasa na tsawon shekaru uku ya barke a shekarar 1967 bayan da jami'an sojojin Igbo suka ayyana kasar Biafra mai cin gashin kanta.

Fiye da mutane miliyan daya ne suka mutu a yakin, akasarinsu 'yan kabilar Igbo - sakamakon yaki da yunwa da cututtuka.

Gwamnatin Najeriya ta haramta kungiyar IPOB, ta kuma ayyana ta a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda tare da zargin ta da haddasa rikicin kabilanci.

~ AFP