Sojojin Masar Sun Ce Sun Tsoma Hannu Don Ceto Kasar

Masu zanga-zanga a dandalin Tahrir a birnin al-Qahira

Sojoji da jami'an jam'iyya mai mulki sun ce shugaba Hosni Mubarak zai biya bukatun masu zanga-zangar neman saukarsa, kuma zai yi jawabi in an jima

Gidan telebijin na Masar yace nan da jimawa a cikin daren alhamis din nan shugaba Hosni Mubarak zai yi jawabi ga al'ummar kasar. Tun da farko a yau din, hafsoshin sojan kasar da kuma jami'an jam'iyya mai mulki sun ce shugaban "zai biya bukatun" masu zanga-zangar neman saukarsa daga kan mulki.

Misrawa sun yi kwanaki 17 su na zanga-zangar neman hambarar da shugaba Mubarak, wanda yayi shekaru kusan talatin yana mulkin kasar. Sun bukaci da ya sauka ba tare da wani jinkiri ba.

A yau alhamis, majalisar koli ta soja ta yi wani taro ba tare da shi shugaba Hosni Mubarak ba, wanda shi ne babban kwamandan sojojin kasar.

Rundunar sojojin ta fito a telebijin tana bayyana cewa tana goyon bayan "halaltattun bukatun jama'ar kasar." Wani kakakin majalisar koli ta sojan yace majalisar tana nazarin matakan da zata iya dauka domin kare kasar da al'ummarta.

An barke da sowa ta murna a fadin dandalin Tahrir, cibiyar wannan zanga-zanga, a lokacin da wannan labari ya bazu daidai faduwar rana agogon kasar.