Sojojin Kasashen ECOWAS Suna Gambia Domin Sharewa Sabon Shugaban Kasar Fage

Tsohon shugaban Gambia Jammeh daga hagu da sabon shugaba Barrow daga dama

A Gambia sojoji daga kasashen ECOWAS sun isa Banjul babban birnin kasar jiya Lahadi, inda dumbin jama'a suka yi masu kyakkywar tarbo da sowa,bayanda shugaban kasar Yahya Jammeh wanda ya sha kaye a zaben kasar yayi gudun hijira.

Ana sa ran rundunar mayaka daga kasashen ECOWAS ko CEDEAO zasu share fage domin komawar shugaban kasar na gaskiya Adama Barrow,wanda tun farko ya sami mafaka a makwabciyar kasa Senegal saboda Yahya Jammeh yaki ya mika masa mulki. A can ne Shugaba Barrow yayi rantsuwar kama aiki a ofishin jakadancin Gambia ranar Alhamis a Daka babban birnin kasar.

Har zuwa daren jiya Lahadi ba'a bada lokacin da shugaba Adama Barro zai koma Gambia ba, amma wani kakakin sabuwar gwamnatin ya gayawa manema labarai cewa hakan zai faru "ba tareda wani bata lokaci ba". Amma wani jami'in ECOWAS Marcel Alain de Souza yace tilas neakwance damarar wani bangaren dakarun kasar kamin Barrow ya koma Gambia.

Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh yana barin kasar

Wani kakaki na biyu ya gayawa manem labarai a Banjul cewa, yau Litinin ake sa ran nazarin ko da akwai wadatacciyar tsaro a babban birnin kasar domin komawar Barrow kasar mai al'uma milyan daya da rabi.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka tayi lale da ci gaba da mika mulki a cikin lumana a Gambia," daga nan ta taya shugaba Barrow murna kan bikin kama aiki da yayi.