Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon shugaban Gambia Jammeh, Yana Gudun Hijira.


Yahya Jammeh yake barin Gambia a daren jiya.
Yahya Jammeh yake barin Gambia a daren jiya.

Jammeh ya bar Gambia a daren Asabar ba tareda yace uffan ba a tashar jirgin sama dake Banjul.

Shugaban Gambia Yahya Jammeh, wanda ya sha kaye a zaben kasar, ya bar kasar a daren Asabar, mataki da ya kawo karshen mulkin kama kariya na shekaru 22, da rikicin siyasa wanda ya kusa jefa kasar cikin rikici da sojojin kasashe da suke yammacin Afirka, karkashin kungiyar ECOWAS.

Shugaba Jammeh baiyi wani bayani ba,lokacinda yake barin kasar a tashar jirgin sama dake Banjul tareda iyalinsa a cikin wani jirgi da bashi lamba. Babu tabbas na inda ya dosa. Yana tareda shugaban Guinea Alpha Conde.

Wannan matakin da shugaba Jammeh ya dauka ya warware barazanar matakin soja wand a ya sami goyon bayan kungiyar tarayyar Afirka da kuma kwamitin sulhu na MDD.

Da tafiyar shugaba Jammeh, hakan ya bada damar mika mulki ga Adama Barrow, wanda ya lashe zaben makonni bakwai da suka wuce.Barrow, wanda yayi rantsuwar kama aiki a ofishin jakadancin Gambia dake makwabciyar kasa Senegal, ranar Alhamis, yanzu ana sa ran zai koma gida.

Ahalinda ake ciki kuma, an kai wani hari d a gurneti a wani ofishin 'Yansanda a yankin Shebelle a Somalia har wani kwamanda daya ya rasa ransa wasu mutane biyu suka jikkata.

Babban jami'in 'Yansanda a yankin MOhammed Siyad Ali wanda ya tabbatarwa MA haka yace, manjo khalif Abdullahi Arfaye ya rasa ransa sakamkon mummunar raunuka d a ya samu ya cika, bayan da aka kai shi asibiti.

Duk da cewa babu wanda ya fito ya dauki aalhakin kai harin , jamia'ai a yankin suna zargin alshaba.

XS
SM
MD
LG