‘Yanjaridan Kurdawa da na kasashen yammacin turai dake hade da sojoji sun ce rundunar na fuskantar cijewa daga mayakan ISIS da suka girka katangun kariya daga hare-hare kuma suka shuka nakiyoyi akan hanyoyi don kawo jinkiri ga dannowar sojojin na Iraq.
Sojin Iraqi sunce yanzu haka wata rundunar mayakansu masu tankunan yaki na can sun danno daga bangaren gundumomin kudu-maso-gabashin birnin, a matsayin wata dabarar kare wasu manyan kauyukka dake yankin da kuma kewayen birnin na Mosul.
Wannan yunkurin kama Mosul din dai da keyi ya zo ne makwanni biyu bayan da rundunar hadin guiwan sojojin Iraqi da Kurdawa dake da goyon bayan mayakan Shi’a da sojojin Sunni da kuma jagorancin Amurka, suka kaddamarda harin da ake cewa shine mafi girma a cikin kasar tun shekarar 2003 don kwato birnin na Mosul daga hannun yan kungiyar ISIS