Kakakin ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon Kyaftin din mayakan ruwa, Jeff Davis yace wannan nasara ya hada da kama garin Bartella mai nisan kilomita 30 daga gabashin Mosul.
Sojojin Iraqi da mayakan Kurdawa na Peshmerga suna kara dannawa ta cikin kananan garuruwa zuwa arewa da gabashi da kuma kudancin Mosul a yayid da suke kusa da birnin kansa da suke kokarin kwacewa.
Sai dai kuma jami’an Amurka sun yi kashedin cewa za a jima ana wannan gwagwarmaya, sannan kuma ana kyautata zaton yakin zai kara karfi a yayinda da sojojin na Kurdawa da Iraq ke ci gaba da dannawa zuwa birnin na Mosul.