Shaidu da bangarorin mayakan kasar Ivory Coast masu jayayya da juna sun fada a yau talata cewa sojojin shugaban da duniya ta amince da shi, Alassane Ouattara, sun kwace garuruwa biyu.
Mayakan Alassane Ouattara sun kwacewa sojojin Laurent Gbagbo garin Daloa na yammacin kasar da kuma garin Bondoukou da ke gabashin kasar.
A jiya litinin kazamin fada ya barke a garin Duekoue mai tarin muhimmanci a dabarun yaki a yammacin kasar wanda kuma ya dade a hannun sojojin Laurent Gbagbo.
Mayakan Alassane Ouattara sun ce sun kama garin, amma a jiya litinin sojojin Gbagbo sun ce da saura dai.
Fadan ya barke ne a daidai lokacin da sojojin Alassane Ouattara su ka kaddamar da hare-hare a yankunan kasar da dama.
'Yan tawaye magoya bayan Alassane Ouattara sun samu dadin gushi a 'yan makonnin nan inda su ka kwace garuruwa biyar a kalla daga hannun sojojin Laurent Gbagbo a yammacin kasar.
Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutanen da yawan su ya kai miliyan daya sun gudu daga gidajen su sanadiyar rikicin da ya biyo bayan zaben kasar Ivory Coast.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce daga barkewar rikicin a cikin watan disemba ya zuwa yanzu, mutane Dari Hudu da Sittin-Biyu (462) aka halaka.