Da alamar dai babu ko duriyar sasantawa a Ivory Coast, akalla zuwa jiya Talata, a sa’ilinda kuma dakarun da ke biyayya ga mutumin da duniya ta ayyana a matsayin shugaban kasar, Alassane Ouattara, su ka kama wasu muhimman garuruwa da dama.
A wani samamen da suka fara tun ranar Litini, mayakan sun kwace garin Bondoukou da Abengourou da ke gabas, da kuma garin Daloa da ke yamman ta tsakiya da garin Duekoue da ke yammacin kasar. Dagan an kuma sabbin dakarun da ke biyayya ga Ouattara suka cigaba da dannawa Kudu zuwa birnin Abidjan.
Har yanzu dai dakarun da ke biyayya ga Shugaba Laurent Gbagbo su ke rike da babban birnin na Ivory Coast. To amman kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito mai magana da yawunsa Ahoua Don Mello na fadi jiya Talata cewa dakarun na Gbago na kiran a tsagaita wuta.
Kamfanin dillancin labaran na AFP ya kuma ce Ouattara ya fiatar da wata takardar jawabi mai cewa an gama bin duk wata hanyar lalama ta ganin Mr. Gbagbo ya amince cewa ya sha kaye.