Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Tawayen Kasar Ivory Coast Sun Danna Zuwa Babban Birnin Kasar


Mayakan da ke goyon bayan Ouattara, rike da makaman su a garin Duekoue, a yammacin kasar Ivory Coast.
Mayakan da ke goyon bayan Ouattara, rike da makaman su a garin Duekoue, a yammacin kasar Ivory Coast.

Fada ya kazance a kasar Ivory Coast inda sojojin Alassane Ouattara ke kara dannawa zuwa Yamoussoukro, cibiyar gwamnatin kasar.

Shaidu sun ce mayakan Alassane Ouattara sun shiga sabbin garuruwa biyu a kalla a yau laraba bayan da a jiya su ka kwace birane da dama daga hannun sojojin shugaba mai ci Laurent Gbagbo.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ruwaito kakakin sojojin Mr. Ouattara, Leon Alla, ya na cewa mayakan su sun kwace garuruwan Bouafle da Sinfra a yankin tsakiyar kasar. Haka kuma shaidu sun bada labarin jin amon bindigogi a garin Tiebissou, da ke tazarar kilomita 40 da Yamoussoukro.

Wani kakakin Mr.Gbagbo mai suna Don Mello, ya yi kira a tsagaita wuta kuma a fara tattaunawa. Ya kara da cewa sojojin Gbagbo za su yi amfani da ‘yancin su na kare kan su wanda ya halasta a gare su.

Akasarin kasashe sun amince da Mr.Ouattara a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka yi a cikin watan nuwamba. Amma Mr. Gbagbo ya ki, ya mika mulki.

Shugaban mai ci Laurent Gbagbo ya na ci gaba da rike birnin Abidjan, wanda shi ne mafi girma a kasar Ivory Coast, kuma cibiyar hada-hadar kasuwanci.

XS
SM
MD
LG