Sojojin Chadi Sun Fatattaki ‘Yan Boko Haram Zuwa Kamaru Da Nijar Da Kuma Najeriya

Sojojin Chadi na kare iyakar Najeriya da Kamaru.

Gwamnatin kasar Chadi ta fada a ranar Talata cewa daruruwan mayakan Boko Haram na ficewa daga yankin tsakiyar Afirka suna tsallakawa zuwa kasashen Kamaru da Nijar da kuma Najeriya.

Gidan talabijin din kasar ya rawaito mayakan sun tsere bayan arangama da sojojin Chadi a karshen mako, wanda ya yi sanadin kashe mayakan Boko Haram sama da 100 da kuma sojojin Chadi kusan 20.

Tashar talabijin ta kasar Chadi ta bayar da rahoton cewa, ana ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin ‘yan Boko Haram, inda sojojin suka sami asarar rayukan kusan sojoji 20, tare da jikkata wasu 32 a wani artabu da suka yi da ‘yan ta’addar Boko Haram a yankin tafkin Chadi a ranar Asabar.

Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta ce kimanin mayakan Boko Haram 100 ne suka mutu, yayin da wasu 100 suka samu raunuka, inda mayakan na Boko Haram ke tserewa zuwa kasashen Kamaru da Najeriya da kuma Nijar.

A farkon watan nan ne sojojin kasar Chadi suka kaddamar da wani farmaki da nufin fatattakar ‘yan ta’addar Boko Haram daga yankunan da ke kusa da tafkin Chadi, a cewar shugaban kasa, Janar Mahamat Idriss Deby.

Deby ya ce farmakin mai suna Haskanite, na zama a matsayin daukar fansar kashe sojojin gwamnati 40 a watan Oktoba, da kuma inganta tsaro ga fararen hula a yankin.

Hare-haren ya haifar da ‘da mai ido a makon da ya gabata, lokacin da Deby ya ce sojojin Kamaru da Najeriya da kuma Nijar, wadanda dukkansu ke ba da gudummawar sojoji ga rundunar hadin gwiwa ta yaki da ta'addanci a yankin, sun yanke shawarar kin hada kai da harin na Chadi.

Kasashen Kamaru da Najeriya da Nijar ba su bayar da wata sanarwa a bainar jama'a ba, da ke tabbatarwa ko musanta ikirarin na Deby ba, kuma Muryar Amurka ba ta iya tabbatarwa da kanta ba, ko kasashen uku sun zabi kin shiga aikin na Chadi.

Sojojin Kamaru sun ce tsaro ne kan iyakokin kasar da kuma kare fararen hula.

Deby ya ce ya shirya janye sojojinsa daga rundunar kasa da kasa da ke da kusan dakaru 11,000, saboda rashin samun abin da ya kira hadin kai tsakanin kasashe mambobin kungiyar na yaki da ta'addancin Boko Haram.

Chadi ba ta bayyana lokacin da za ta janye sojojinta daga rundunar hadin gwiwa da ke samun taimakon Majalisar Dinkin Duniya ba.

A shekara ta 2009 ne kungiyar Boko Haram ta kaddamar da tawaye da makamai ga gwamnatin Najeriya, domin kafa daular Musulunci. Tun daga lokacin yakin ya bazu zuwa kasashe makwabta kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 40,000 tare da raba sama da miliyan 3 da muhallansu a cewar Majalisar Dinkin Duniya.