Hukumar bayar da umurni ga sojojin Amurka, dake yankin ta fadi cewa a yayin samamen na yau Talata a jahar Marib, sojojin Amurka sun yi amfani da jiragen yaki da kuma kananan makamai wajen hallaka mayakan a wani rukunin gidaje mai alaka da AQAP.
"Samame irin na taimakawa wajen gane shirye-shiryen, da karfi da kuma manufar AQAP, wanda hakan kan taimaka mana wajen cigaba da farautowa da birkitawa da kuma nakasa AQAP," a cewar wata takardar bayani daga CENTCOM.
Amurka, ta ce ta dau wannan matakin sojan ne tare da goyon bayan gwamnatin Yamen. A watan Maris ma Amurka ta kai hare-hare da jiragen yaki da jirage marasa matuka a kan AQAP a wasu sassa na Yemen.
Haka zalika a watan Janairu wasu sojojin kundunbalar Amurka, sun kai samame kan wani rukunin gidajen AQAP, matakin sojan da ya yi sanadin mutuwar sojan ruwan kundunbalan SEAL William Ryan Owen.
Cikin wadanda su ka mutu a yayin wannan samamamen, har da Nawar Anwar al-Awlaki, wata ba-Amurka 'yar shekaru 8 da haihuwa, diyar marigayi Anwar al-Awlaki, wani ba-Amurken malami mai tsattsauran ra'ayi, wanda shi kansa aka kashe da jirgi mara matuki a shekara 2011.