Sojojin Amurka fiye da 100 ke dafawa sojan Iraq da na Kurdawa da ke ci gaba da kutsawa a kokarin da suke na sake kwace muhimmin garin nan na Mosul daga hannun mayakan ISIS.
WASHINGTON, DC —
A jiya Talata ne wani kakakin ma’aikatar tasron Amurka ta Pentagon, Kyaftin Jeff Davis yake gayawa manema labarai cewa wadanan sojan na Amurka suna tafiya ne tare da mayakan Kurdawa kamar dubu 10 da sojan Iraq su kamar dubu 18 da tarin ‘yansanda dake shirin fuskantar dimbin mayakan ISIS wadanda suka yi kwantan bauna a cikin birnin na Mosul, garin da suka share fiye da shekaru biyu a cikinsa, suna jiran isowar abokan fadan nasu don a gwabza.
Koda yake ana jin mayakan ISIS dake Mosul basu shige tsakanin 3,000 zuwa 5,000 ba, an san cewa su gwanayen mazan yaki ne ‘yan gani-kashe-ni, kuma sunfi sadaukar da kai kana sun fi rawan jikin son a zo ayi yakin da su.