Sojojin Amurka Na Neman Hanyar Sulhu Da Rasha Kan Syria

Sojojin Amurka sunce suna nan suna iya bakin kokarin su, na ganin sun kara samar da hanyar da zata rage yiyuwar fito na fito da kasar Rasha akan maganar Syria.

Sai dai abin da ba a sani ba shine ko sojojin kasashen biyu suna amfani da sanannun layukan sadarwa da suke dashi domin kaucewa hadarin jiragen saman su a sararin samaniyar kasar Syria.

Babban mai magana da yawun askarawan tsakiya ta sojan saman Amurka, Kanar John Thomas, ya shaidawa manema labarai jiya littinin cewa Sojojin Amurka sun sanar da Kasar Rasha cewa Amurka na shirin kaiwa Syria hari a matsayin ramuwa ga harin makami mai guba da sojoji Syria suka kai wa wasu farar hula wanda yayi dalilin mutuwar farar hula har sama da 80.

Thomas yace kuma hanyar sadarwan da rundunar ta saba anfani da ita, da ita tayi anfani wajen aikawa da wannan sakon kuma ba alamar cewa sakon bai tafi ba.

Sai dai Kanar Thomas yace ba zasu bayyana hanyar da zasu bi na tattauna wannan batu ba a halin yanzu har sai sunga abin da hali yayi.

Sai dai a bangaren ta, Rasha tace tuni ta dakatar da amfani da wadannan hanyoyin sadarwan a matsayin nuna fushin ta akan harin da aka kai a ranar 6 ga wannan watan, a sansanin Al-Shayrat, wanda aka kai da makaman nan kirar Amurka da ake kira Tomawalk.