Sojojin Ambazoniya Daga Kamaru Sun Kashe Wani Sarki a Jihar Taraba

Wasu da ake zargin yan aware masu fafutukan kafa kasar Ambazoniya sun kai hari wani gari da ke kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Kamaru dake karamar hukumar Takum a jihar Taraba.

Mharan sun kuma kashe sarkin da mutane sama da biyar a wannan yankin.

A cikin hirar shi da Muryar Amurka, Shugaban karamar hukumar Takum ya tabbatar da aukuwar lamarin da ya ce ya faru ne a iyakan su da jamhuriyar Kamaru inda 'yan awaren suka aikata wannan mummunarn harin kuma suka kashe mutane biyar, ciki harda sarkin.

Mai magana da yawun kakakin rundunar yan sanda jihar Taraba DSP Usman Abdullahi, ya ce suna bakin daga domin ganin a kawo karshen wannan mastalar da kuma tabbatar da wadanda suka riga suka rasu sakamakon wannan tarzoman a wannan yankin.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Sojojin Ambazoniya Daga Kamaru Sun Kashe Wani sarki Da Mutum 11 A Taraba

Inganta Tsaro

Your browser doesn’t support HTML5

Jami’an Tsaron Najeriya Sun Gudanar Da Tattakin Hadin-Gwiwa