Kazalika gwamnatin kasar ta Kamaru ta ki amincewa da muradun 'yan bangaren kasar dake anfani da harshen Ingilishi inda suka bukatan neman canza tsarin mulkin kasar daga jamhuriya a koma gwamnatin tarayya.
Yankin Ingilishin ya bada zabi. Idan ba za'a koma gwamnatin tarayya ba to a basu nasu 'yancin. Kawo yanzu ma har sun fitar da tutarsu mai alamar fari da shudi kuma sun sanyawa kasar tasu sunan Ambazoniya.
Malam Abdulkadiri Muhammad mai bada shawara a hukumar sadarwa ta kasar Kamaru yace an katse hanyar sadarwan ne na wani dan lokaci bisa ga doka saboda bincike ya nuna rikicin yankin wasu 'yan kasashen waje ne ke haddasashi.
Yace daga waje ana anfani da yanar gizo ana zugasu, ana harzukasu maimakon a bari a sasanta cikin ruwan sanyi a gida. Matsala ce ta 'yan Kamaru su ne kuma ya kamata su cimma masalaha ba tare da tsoma bakin wasu daga waje ba.
Inji Malam Abdulkadiri yanzu haka an samu ana tattaunawa tsakanin masu fushi da wadanda ake fushi dasu.
Acewar Abdulkadir maganar tayi nisa har mutanen waje sun buga ma sashen Ingilishi tuta da kundun tsarin mulki abun da ya nuna ana son a raba kasar. Yace ahalin yanzu Afirka bata son ta ga an yayyana wata kasa kuma.
Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.