Sojoji Sun Tafi da Wasu Mai’aikatan Daily Trust

Sojojin Najeriya (File Photo)

Wasu sojoji daga shiyya to bakwai ta rundunar sojojin Nigeria sun kusa cikin ofishin ‘yan jarida nan ta Daily Trust, inda suka tafi da mai’aikatan jaridar su biyu domin amsawa babban Kwamandan sojojin na shiyyar. Babban edita na Daily Trust ya baiyana abin da ya faru da cewa, sojojin sun zo karkashin jagoranchin sabon mataimakin kakakin shiyyar, wato kanar Sani Usman wanda basu same shi a ofishinsa ba, don haka suka dauki ma’aikatan jaridar mutum biyu gaban shi kwamandan shiyyar, in da aka bukaci jaridar da ta janye wannan labarin. Babban editan Malam Hamza Idris yakare da cewa duk abin da suka rubuta da kuma kafofin da suka basu wannan labarin, suna matukar kokarinsu wajen ganin sun tabbatar da sahihancin labaran dakuma bawa kowa damar fadin nashi ‘bangaren.

A jiya Alhamis ne wasu sojoji daga shiyya ta 7 ta rundunar sojojin Najeriya mai hedkwata a Maiduguri, sun kutsa kai cikin ofishin ‘yan jaridar nan ta Daily Trust, inda suka tafi da wasu ma'aikatan jaridar biyu domin amsa tambayoyi a gaban babban kwamandan shiyyar.

Da alamun rundunar sojojin ba ta ji dadin wani labarin da jaridar ta Daily Trust ta buga a ranar laraba ba, inda ta yi maganar wasu sojojin da suka yi tawaye, bayan da aka tura su bakin daga zuwa garin Bama daga inda zasu shige kwato garin Gwoza. Jaridar ta ce sojojin sun ce ba zasu tafi ba har sai an ba su makamai masu karfi, haka kuma matan sojojin sun futo sun yi bore har da kona tayoyi suna cewa bazasu bar mazajen su tafi yaki batare da amba mazansu ishashshun kayan ai’ki na zamani ba.

Da yake bayyana abubuwan da suka faru, babban editan jaridar Daily Trust mai kula da jihohin arewa maso gabas, Malam Hamza Idris, wanda ya rubuta labarin, yace sojojin sun zo karkashin jagorancin sabon mataimakin kakakin shiyyar, Kanar Sani Usman, amma ba su same shi a ofishin ba.

Don haka suka tafi da wasu ma'aikatan guda biyu gaban shi babban kwamandan shiyyar, inda aka bukaci jaridar da ta janye wannan labarin.

Malam Hamza Idris ya kare labarin da suka rubuta da kuma kafofin da suka ba su wannan labarin, yana mai fadin cewa jaridarsu tana bakin kokarinta wajen tabbatar da sahihancin labarai tare da ba kowane bangare damar fadin abin da ke bakin shi.

Ga rohotan Haruna Dauda Biu.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojoji Sun Tafi da Wasu Mai’aikatan Daily Trust - 4'46"