Tawagar ta BBOG ta hada da jagorarsu Oby Ezekwesili da Hajiya Aisha Yusuf da Manaseh Allen da Ibrahim Usman.
A cewar Ministan yada labarun Najeriya Lai Muhammed ziyarar ta tsawon wuni biyu ce kuma jirgin dake dauke dasu zai yi shawagi dasu akan dajin Sambisan.
Baicin wakilan kafofin labarai mallakar gwamnatin Najeriya akwai kuma wakilan dillancin labarai na kasashen ketare da suka hada da Reuters da AFP.
Wannan ziyarar gani da ido ita ce ta farko da aka gayyaci 'yan gwagwarmayar BBOG amma dama can manema labarai da hedkwatar tsaro sun saba shirya irin wannan ziyarar.
Sanya 'yan BBOG a wannan karon yana da alaka ne da yadda 'yan kungiyar ke nuna rashin gamsuwarsu da bugun kirjin da sojoji keyi na cewa sun wargaza tungar 'yan Boko Haram dake dajin Sambisa. Kungiyar na ganin idan ikirarin sojojin gaskiya ne to yaya aka yi ba'a samo ko daya daga cikin 'yan matan 195 ba? Haka kuma abun mamaki ba'a gano madugun 'yan ta'adan ba Abubakar Shekau wanda kusan kullum yana magana.
A cewar daya daga cikin jigajigan kungiyar BBOG Dr. Emmanuel Shehu har yanzu jami'an tsaron Najeriya basu fahimci abun da ake nufi da dimokradiya ba. Har yanzu suna nan da tunanen lokacin da sojoji suka yi mulkin kasar. Yace saboda haka akwai sauran aiki a kasar musamman akan yadda yakamata jami'an tsaro suyi mua'amala da mutanen kasarsu a karkashin mulkin dimokradiya.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5