Sojoji Sun Gujewa 'Yan Boko Haram da Suka Yiwa Madagali Kawanya

Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram

Jama'ar karamar hukumar Madgali dake jihar Adamawa na zaman zullumi biyo bayan kawanyar da 'ayan kungiyar Boko Haram suka yiwa yankin tare da kafa tutotcinsu.

Lamarin ya sa dimbin jama'a suka kauracewa gidajensu a yankin.

Wani ganao yace 'yan bindigan sun shiga garin Madagalin. Maharan da suke da motocin hilux da motocin sulke sun karbe garin. Wani kuma yace sojojin Najeriya dake yankin sun yi ta kare.

Shugaban karamar hukumar Madagalin James Abawa Watanda ya tabbatar da hakan ya faru. Yace al'ummomin yankin na cikin mawuyacin hali domin rashin sanin abun da ka faru. Da aka tambayaeshi batun sojoji sai yace a bar maganarsu kuma shi ba zai yi maganar sojoji ba. Mr. James yace abu ya gagara babu abun da za'a iya yi yanzu.

Sabili da babu yadda za'a shiga garin ba'a san ko mutane nawa ba ne suka rasa rayukansu. Samun kidigdiga na da wuya yanzu.

Kawo yanzu dai hukumomin tsaro a jihar ta Adamawa basu ce komi ba.

Wani masanin harkokin tsaro Dr Abdullahi Wase yace akwai abun dubawa akan matsalar tabarbarewar tsaro a arewa maso gabas. Yace abun da ya faru tuni ne game da abun da suka kwashe shekaru biyar suna fada cewa akwai lauje cikin nadi. Idan da ma an fara da sunan Boko Haram ne to yanzu hangen mutane ya wuce nan. Duk yadda ake ciki akwai makarkashiya. Akwai wadanda suke son cimma burinsu a zaben 2015. Ban da haka akwai hannun mutanen waje wadanda suka dade suna cewa Najeriya zata wargaje a shekarar 2015.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojoji Sun Gujewa 'Yan Boko Haram da Suka Yiwa Madagali Kawanya - 2' 42"