Rundunar Sojojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole ta kafa wani kwamiti mai mutane hudu da zai binciki musababin harin da aka kai wasu kauyuka dake kewaye da Maiduguri ranar Lahadi.
Harin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikata wasu fiye da saba'in.
Kwamiti din shi ne irinsa na farko da za'a kafa a karkashin kwamandan rundunar Manjo Janar Rogers Nicholas. Ya kafa kwamitin domin bincikar ababen dake faruwa musamman ma hare-haren kunar bakin wake.
A cewar Manjo Janar Nicholas an kafa kwamitin din ne domin ya binciki lamarin da yadda maharan suka shigo inda suka yi aika-aikar. Binciken zai gano yadda za'a hana aukuwar duk wani hari saboda rundunar ta yi ikirarin karya lagwan 'yan Boko Haram..
Inji Manjo Janar Nicholas kwanakin baya sun samu inda 'yan ta'addan ke fakewa har sun kashe bakawi ciki sauran kuma suka kama gudu tare da yin harbe harbe da suka tsorata mutane. A harin ya ce mutane 19 suka mutu da soja daya wanda ya je neman wani abu kana fiye da 70 suka jikata.
Kwamitin mai mutane hudu an bashi kwana uku ya yi aikinsa ya mika rahoto. Birgediya Janar Tafida shi ne shugaban kwamitin ya ce zasu je inda lamarin ya faru su yi tambayoyi.
Haruna Dauda na da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5