Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yin Afuwa Ga Boko Haram Zai Amfani Najeriya – Gwamnati


Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.
Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.

Yayin da hukumomin Najeriya ke laluben hanyoyin da za su kawo karshen rikicin Boko Haram da ya ki ci ya ki cinyewa, Fadar shugaban kasar ta ce yin afuwa ga mayakan kungiyar zai iya zama alheri ga Najeriya.

Fadar shugaban kasar Najeriya ta Aso Rock a Abuja, ta ce yin afuwa ga mayakan Boko Haram zai amfani kasar ta fuskoki da dama.

Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, mai bai wa shugaba Buhari shawara a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya ce shirin afuwar zai iya sa mayakan su ajiye makamansu.

Ya kara da cewa shirin zai taimaka wajen rage yawan kudaden da ake kashewa domin samar da tsaro da kuma rayukan da ake asara.

A baya gwamnatin ta Najeriya, ta taba ta da wannan batu na afuwa amma kuma lamarin bai yi wu ba.

Akwai rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yan Najeriya kan a yi wa mayakan na Boko Haram afuwa ko kuma akasin hakan.

Gwamnatin marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua ta taba yi wa kungiyoyin tsagerun yankin Niger Delta afuwa, domin su ajiye makamansu.

Rikicin Boko Haram ya faro ne tun daga 2009, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da raba wasu miliyoyin da muhallansu a wasu kasashen da ke yankin Tafkin Chadi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG