A Jamhuriyar Nijer sojoji masu tarin yawa sun halaka bayan da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta akan wani ayarin motocin sintiri a kewayen kauyen Tongo Tongo da yammacin jiya, a dai dai lokacin da suka taka nakiya.
Lamarin, wanda ke tattare da abin al’ajabi, ya faru ne a wajejen karfe uku na ranar jiya Talata a kauyen Baley Beri, kusa da garin Tongo Tongo, daura da iyakar Nijer da Mali.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar da faruwar wannan al’amari da ya haddasa asarar rayukan dakaru masu tarin yawa, koda yake kawo yanzu ba a tantance adadin wadanda suka rasun ba ballanatana a fitar da alkaluma inji ta.
Jim kadan bayan kai wannan hari, jiragen sojan saman Amurka da Faransa da Nijer sun garzaya wurin da abin ya faru da nufin fafatakar wadanan mahara sai dai har a zuwa wannan lokacin bayanai na nuna cewa ba daya daga cikin jiragen uku da ya gano inda suka dosa, abinda ya sa ake ganin akwai alamun gamin bakin wasu mazaunan karkarar da aka yi wannan gumurzu, inji wannan majiyar.
Kauyen Tongo Tongo, nan ne inda wasu sojojin Amurka 3 da na Nijer 2 suka hadu da ajalinsu a watan Oktoban 2017, lokacin da wasu ‘yan takife suka yi masu kwanton bauna, lamarin da wani bincike ya tabbatar da gano wasu mazaunan garin da hada baki da ‘yan bindiga.
Yankin Tilabery, mai makwabtaka da kasashen Mali da Burkina Faso, na fama da hare haren ta’addanci a ‘yan makwannin nan, domin ko a shekaranjiya Litinin ‘yan bindiga sun bakunci garuruwan Mangaize da Dolbel, inda suka harbi wani limamin krista a kai yayinda suka yi yunkurin kutsawa gidan yarin Koutoukale. Sai dai jami’an tsaro sun fatattake su koda yake 1 daga cikin dakarun na Nijer ya hallaka sanadiyyar barin wutar.
Ga cikakken rahotun daga: Souley Moumouni Barma
Your browser doesn’t support HTML5