Sojin Saman Najeriya Sun Hallaka 'Yan Bindiga Kusan 100 a Jihar Zamfara

  • Murtala Sanyinna

Operation Dirar Mikiya

A yayin da hare-haren ‘yan bindiga suke kara uzzura a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya, rundunar sojin saman kasar ta ce ta kai wani mummunan hari ta jiragen sama, wanda yayi sanadiyyar hallaka ‘yan bindiga kusan 100, da kuma wargaza sansanoninsu kusan 7 a jihar. 

Daraktan watsa labarai na rundunar sojin saman Najeriya Air Commodore Ibikunle Daramola, ya bayyana cewa an kai farmakin ne domin sa kafar wando daya da ‘yan tada kayar baya, da wargaza sansanoninsu domin samar da zaman lafiya a yankin.

Daramola ya ce an kai farmakin mai take ‘OPERATION WUTAR DAJI 2’ da ke karkashin ‘Operation Hadarin Daji’, a dazukan Damborou, Kwuyambana, Dutsen Asolavda kuma Duten Bagai.

Babban Hafsan Sojin Saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar wanda yanzu haka yake yankin, ya ce suna samun nasarori a farmakin da suke kai wa kan sansanonin ‘yan bindigar a jihar ta Zamfara.

Hafsan Sojin Saman Najeriya Sadique Abubakar tare da Shugaba Muhammadu Buhari

Abubakar ya ce suna amfani da na’urori da ke gano dukkan maboyar ‘yan ta da kayar bayan, wanda hakan ya ba su damar wargaza su.

Gwamnatin Jihar zamfara ta bakin kakakin gwamnan jihar Zailani Baffa, ta bayyana gamsuwa da yadda sojojin suke ci gaba da aikin fatattakar ‘yan bindigar da suka hana jama’a walwala a jihar.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:

Your browser doesn’t support HTML5

Sojin Saman Najeriya Sun Kashe Akalla 'Yan Bindiga 100 A Zamfara