Rundunar sojin Najeriya ta ce ta hallaka akalla ‘yan bindiga 58 a yanin jihar Zamfara, yayin wata arangama da ta auku tsakaninsu da ‘yan bindigar.
Wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakin jami’in yada labarai na rundunar, Major Clement K. Abiade, wacce aka fitar a yau Laraba, ta nuna cewa, an yi arangamar ce a ranar 20 ga watan Janairu.
“Wadanda suka jikkata a bangaren ‘yan bindigar mutum 58 ne, sannan an kama mutum guda da ransa, sannan mun tarwatsa wasu sansanoni 18 kana muka kubutar da wasu mutum 75 da ake garkuwa da su,” a cewar Abiade.
Akalla sojojin Najeriya biyu ne suka rasa rayukansu, kana wasu 'yan vigilante biyu su ma sun mutu.
Sanarwar ta kara da cewa, wadanda aka kubutar, mutane ne da aka yi garkuwa da su domin neman kudin fansa, kuma tuni an sake hada su da iyalansu.
Rundunar sojin ta Najeriya ta ce, ta kuma karbe makamai da dama daga hannun ‘yan bindigar da suka hada da bindiga kirar AK 47 guda hudu, dumbin harsashai da kuma Baburan guda 40.