Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kubutar Da Mutune 18 A Jihar Zamfara


Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kubutar da mutune 18 daga hannu 'yan bindiga akan hanyar Maru da garin Dansadau dake jihar Zamfara.

Hakazalika rundunar sojin tayi nasarar hallaka ‘yan fashi guda 10, ciki harda da wani gagarumin dan fashi da ake kira Alhaji, wanda ya dade yana addabar mutane a yankin.

A karin bayanin da yayi, Jami’in sadarwa na aikace-aikace a shelkwatar tsaron Najeriya, Navy kwamanda Abdulsalam Sani, ya ce a cikin mutanen da sojojin suka kubutar sun hada da maza goma, mata hudu, sai yara kanana su hudu.

Sakamakon wani hari na kawar da 'yan bindiga da kuma tsare al’umma da dukiyoyinsu da rundunar sojoji ta 31 ta kai a dajin Dogon Gona dake jihar Niger, ta samu nasarar kubutar da wasu mutane bakwai da akayi garkuwa dasu tun ranar 27 ga watan Maris.

Hakazalika sojojin sun fafata da wasu ‘yan bindiga a kauyen Kontokoro dake jihar Niger, yayin da suka kashe ‘yan bindiga da dama.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG