Wannan shi ne harin farko kai tsaye da Amurka ta kai ga sojojin gwamnatin Syria. Jerin makamai masu linzami kirar Amurka, sune aka yi anfani da su wajen kai wannan harin daga sansanin sojan ruwan Amurka, dake tekun Bahar-Rum.
Ana kyautata zaton wadannan makaman sun sauka dai-dai inda aka auna su, a kudancin kasar akan sansanin sojan saman Syria.
Wannan harin dai ramuwa ce ta harin makami mai guba, wanda jami’an Amurka, suka yi imanin cewa sojojin gwamnatin Syria, sun kai a wurin da ‘yan tawaye ke rike da shi a kasar ta Syria.
Jim kadan da kai wannan harin shugaba Donald Trump, ya shaidawa manema labarai cewa shine ya bada umurnin kai wannan harin
Shugaban yana Magana ne a wurin da ya tafi shakatawa na karshen mako a gabar Tekun Florida.
Yace nayi haka ne domin jaddada matakan tsaron Amurka, Kana ya bayyana harin na makami mai guba a matsayin aikin dabbanci, domin ko wannan yayi dalilin salwantar da rayukan bayin ALLAH, maza da mata da yara.