Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Trump Ta Jingine Batun Raba Iyali Marasa Takardun Izinin Shiga Amurka


Gwamnnatin shugaba Donald Trump, ta jingine barazanar da ta yi cewa zata raba duk wasu iyalan da suka kama suna tsallaka bakin iyakar Amurka, da Mexico, domin shigowa cikin Amurka.

Jiya ne Ministan harkokin cikin gida Jonh Kelly, ya shaidawa majilisar dattijai cewa, ba za a raba uwa da ‘ya’yanta ba, sai dai idan ya zame ba wani zabi na yin hakan.

Yace misali inda aka samu iyayen basu da lafiya ko kuma an same su da laifin zamowa mashaya, musammam shan kwaya ba bisa ka’ida ba.

Amma dai ma’aikatar tsaron ta cikin gida tace za a raba iyalan da aka samu zasu shigo Amurka, ba bisa ka’ida ba idan daga kasashen yankin nahiyar tsakiyar Amurka, suka fito.

Kelly ya shaidawa sanatocin cewa sake wannan manufar gwamnati ya biyo bayan raguwar adadin kame bakin haure a cikin shekaru 17 da suka gabata, yace a cikin watan da ya gabata an samu kasa da dubu 17 sabanin abinda ake samu ada.

Yace ba shakka munga raguwar bulbulowar bakin hauren daga yankin kasashen Amurka, ta tsakiya zuwa cikin Amurka. Kelly yace hakan y faru ne saboda kalaman shugaba Donald Trump, ciki har da batun kame bakin haure masu shigowa Amurka, ba bisa ka’ida ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG