Sojan Nijer Sun Kashe 'Yan Ta'adda 10 A Kauyen Tchomabangouna Jihar Tilabery

NIAMEY

Dakarun tsaron jamhuriyar Nijer sun hallaka gwamman ‘yan ta’adda a yammacin jiya lahadi lokacin da suka kai hari a kauyen Tchomabangou dake jihar Tilabery koda yake sojoji 4 da fararen hula 5 sun rasu a yayin wannan arangama.

‘Yan bindiga sama da 100 da suka zo akan babura dauke da manyan bindigogi ne aka bayyana cewa sun afkawa kauyen Tchomabangou a wajejen karfe 3 na ranar jiya lahdi.

Martanin da askarawan Nijer suka mayar a take ya basu damar fatatakar wadanan mahara. Sakamakon wucin gadi na cewa ‘yan ta’adda 40 sun sheka lahira yayinda jami’an tsaro 4 da fararen hula 5 suka kwanta dama sai wasu soja 3 da suka ji rauni sanadiyar wannan al’amari a cewar sanarwar da ministan tsaro Alkassoum Indatou ya fitar wace ta kara da cewa, askarawan Nijer sun karbe babura 14 manyan bidigogin kirar 12 7 biyu (2) da PKM 2 da RPG 7 hudu(4) sai bingogin AK 47 goma sha biyu (12) da wata samfarin MAS 36 guda(1) sai wasu wayoyin Motorola kimanin 10.

Tsohon ministan tsaron kasar Nijer kuma dan majalisar dokokin kasa Kalla Moutari na cewa wannan labari na da dadin ji.

Garin Tchomabangou na daga cikin garuruwan da ‘yan ta’adda suka karkashe fararen hula sama da 100 a farkon shekarar da muke ciki. A washegarin faruwar wannan al’amari gwamnatin Nijer ta karfafa matakai domin tabbatar da tsaro a irin wannan wurare masu makwaftaka da kasar Mali. shugaban kungiyar voix des sans Voix Alhaji Nassirou Saidou na cewa..

A yayin wani taron manema labarai na hadin guiwa da takwaransa Emmanuel Macron na Faransa Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya bayyana cewa yakin da ake kwafsawa da ‘yan ta’’adda a yankin sahel wani abu ne da sojojin cikin gida zasu iya karewa da shi a dan kankanen lokaci muddin aka basu kayan aiki irin na zamani saboda haka tallafin jiragen sama da bayar da bayanan sirri shine abinda ya fi dacewa Faransa ta bayar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Sojan Nijer Sun Kashe 'Yan Ta'adda 10 A Kauyen Tchomabangouna Jihar Tilabery