Wasu ‘yan bindiga sun kai wa wani karamin sansanin sojojin Najeriya da ke jihar Neja hari.
Da asubahin ranar Laraba ‘yan bindigar suka aukawa sansanin da ke garin Zazzaga a yankin karamar hukumar Sarkin Fawa da ke jihar.
Shaidu sun ce maharan sun kona motar sojojin tare da yin awon gaba da wata motar sannan wani soja guda ya yi batan dabo.
Wasu rahotannin sun ce maharani sun kuma kona rumbun adana abinci da ke barikin sojin.
Karin bayani akan: jihar Neja, Nigeria, da Najeriya.
Babu dai rahotannin da ke nuna cewa an samu asarar rayuka daga bangaren sojojin kasar, amma akwai bayanai da ke nuni da cewa an jikkata maharan da dama.
Kawo lokacin hada wannan rahoto dai babu wani cikakken bayani daga bangaren Jami'an tsaron akan wannan sabon hari.
Amma Kwamishinan labarai na jihar Nejan Alh. Sani Idris ya tabbatar wa da Muryar Amurka aukuwar wannan hari.
Kuma ya ce gwamnatin Jihar Nejan na iya kokarinta wajen shawo kan matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar Neja.
A ‘yan kwanakin nan dai kusan kullum sai maharan sun kai hari akan jama’a a jihar wacce ke tsakiyar arewacin Najeriya.
Neja ta hada iyaka da jihohin Kaduna daga gabashi, Kebbi da Zamfara daga arewaci, wadanda duk jihohi ne da ke fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga.