Aminu Mahi matashi kuma dan gwagwarmayar kwatowa matasa 'yanci a fannin siyasa, ya ce harka ta Iyayen gida a fannin siyasa a wannan gwamnati za’a iya cewa ta dan kau. Domin kuwa an bawa matasa dama amma basa damawa yadda aka so, domin kuwa da dama ikirarin matasa kenan na cewar ba’a damawa da su kamar yadda ake damawa da mata.
Amma abin takaici a yanzu da aka basu damar har aka sa wasu matasan a wasu madafan ikon, suna barin turbar da aka dorasu domin su wakilci yan uwansu matasa, da zarar sun dare kan kujerar iko sai alkalumma su canza maimakon yayi kokarin cusa akidun matasa.
Ya ce da yawa daga cikin matasa da suka samu dama suna kokarin gina kawunansu ne, sabanin akidun da suke da su kafin su sami wata madafar iko, ya kara da cewa watakila rudewa suke yi ko kuwa suna ganin abinda basu taba gani ba ne, Allah masani a cewar Aminu Mahi.
Matashin ya ce wasu ko da an zauna da su sai su ce matasa ba zasu gane ba, ba haka abin yake ba, sai tunaninsu ya sauya irin na iyayen gidansu tare da cewa abin takaici sai matasa su canja akalarsu, a cewarsa kamar ko system ne ke juya matasa maimakon matasan su juya system wato tsarin tafiyar da mulkin.
Aminu Mahi, ya ce a yanzu duk wanda ke da niyyar takara ko makamanci haka sai sun tabbatar sun tattance matashi ta sanin irin taimakon da yake baiwa alummarsa, ko kuma ma ya bayyana irin taimakon da yayi a ma gidansa kafin ya yi tunani kawo canji ga 'yan uwansa matasa.
Kadan kenyan daga cikin hirarmu da matashi dan gwagwarmaya Aminu Mahi, ku biyo mu domino jin cikakkiyar hirar mu da shi.
Your browser doesn’t support HTML5