Jamila Ado Mai Wuka ta sake ziyarta DandalinVOA inda a wannan lokaci ta ce ta sauya salon wakarta daga wakar Nanaye zuwa wakokin al’adu irin na da duba da gushewar al’ada tsakanin matasa.
Ta ce ta fara wannan waka ne domin ta nusar da ‘yan uwanta mata alfanun raya al’ada kowacce al'umma, a cewarta al’adar al’umma ita ce al'umma
Jamila ta kara da cewa wakar ta tana maida hankali ne wajen fito da suturar al’ada, abinci da sauransu sannan tana fito da wasu kalmomi da a yanzu mafi yawan matasa basu sansu ba.
Matashiyar ta ce da waka ne take koyar da zanci ko Karin Magana da isar da sako a cikin nishadi baya ga wa’azantarwa da fadakarwa.
Daga karshe ta ce babban burinta ta sami daukaka kowa ya santa inda ta ce tana waka ba don ta samu kudi ba illa tayi suna a santa asssan duniya da dama.
Facebook Forum