Wani tsohon gwamnan soja a Jihar Kaduna, kuma jigo a kungiyar kare muradun yankin arewacin Najeriya, Kanar Hamid Ali mai ritaya, yace siyasa ce kawai ta sanya aka jefa sojojin Najeriya cikin halin da ya sa ba su iya yaka ko tare 'yan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.
Kanar Hamid Ali, yace sojojin Najeriya kwararru ne wadanda suka yi yakin basasa, da kuma yake-yake a kasashe irinsu Kwango, inda yake da sunkuru mai yawa, da wasunsu, kuma duk inda suka je sun yi tasiri sosai.
Yace amma an wayi gari a cikin kasarsu ma, kuma a inda ma ba wani daji mai sunkuru ba ne, amma sun gagara tabuka komai. Yace da ma abinda ya raba soja da farar hula shi ne makami, da kuma horaswa ta aikin soja. Yace muddin soja ba ya da makami, babu ta yadda zai iya samun galaba.
Yace alhakin gwamnati ce ta sayi makamin yaki, ba shi soja ba, tunda ba zai iya zuwa kasuwa yace zai sayi makamin fada ba. Don haka yace idan gwamnati ba ta yi niyya ba, babu inda soja zai samu makami.
Kanar Hamid Ali yace a bayan rashin makiamai ma, yanzu sojojin Najeriya ba a kulawa da su yadda ya kamata.
Yace wannan abin duk ya samo salsala ne daga siyasa, idan gwamnati tana son kawo karshensa, zata iya tuni. Amma da yake zaben 2015 ya kusa, watakila ana kara barin wannan abu yana tabarbarewa ne ta yadda ba za a iya gudanar da zabubbuka a wasu wuraren da gwamnatin take ganin zata fadi ba.
Your browser doesn’t support HTML5