Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya na Fuskantar Karin Suka Saboda Gaza Murkushe Boko Haram. Amma su Kan ce ba Laifinsu ba ne


Wasu sojojin Nijeriya a bakin aiki.
Wasu sojojin Nijeriya a bakin aiki.

Ganin yadda 'yan Boko Haram ke ta kwace garuruwa a arewa maso gabashin Nijeriya; 'yan Nijeriya daidaiku da kungiyoyi sun tashi haikan wajen sukar sojojin Nijeriya da kuma hukumomin da alhakin wadata sojin da makamai ya rataya a wuyarsu. To saidai kuma, su ma su na ikirarin cewa ba laifinsu ba ne.

Yayin da ‘yan kungiyar Boko Haram ke ta kara kwace garuruwa a arewa maso gabashin Najeriya, wasu kungiyoyi da daidaikun ‘yan Nijeriya na ta kiraye-kirayen a kara yawan sojoji a kuma ba su ingantattu kuma isassun makamai. To saidai wasu a bangaren gwamnati ciki har da mai taimaka ma Shugaban kasa na musamman Doyin Okupe ya ce ya kamata jama’a su gane cewa ba wai sojojin Najeriya sun gaza ba ne. Yaki da ‘yan sari ka noke abu ne mai waya.

Idan ba a mance ba dai, Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya Alhaji Suleiman Abba, ya ce har yanzu ana neman ‘yan sanda kimanin 20 da su ka bace tun lokacin da ‘yan Boko Haram su ka nemi kwace garin Gwoza mai cibiyar horar da ‘yan sandan kwantar da tarzoma. Shi kuwa Alhaji Musa Yola, wani shugaban Al’umma da ke Yola cewa ya yi rashin bai wa sojoji isassu kuma ingantattun kayan yaki ne musabbabin gazawar sojin Najeriya. Don haka ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dau matakan da su ka dace na wadata sojoji da kayan yaki.

To saidai kuma a nasa martanin, kakakin sojin Najeriya Manjo Chris Olukolade ya musanta zargin cewa al’mundahana da kuma danne hakkin kananan sojoji na taka rawa wajen gazawarsu.

XS
SM
MD
LG