Biyo bayan sanarwar da jakadan Jamus dake Nijar ya fitar makon jiya sai gashi shugaban kasar ta Jamus Angela Merkel ta fara ziyarar Nijar din yau Litinin.
Su dai 'yan Nijar mazauna Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu akan wannan ziyara ta shugabar Jamus. Wasu sun tuna da aikin noman rani da kasar Jamus tayi a jihar Agades da har yanzu suna cin moroyarshi. Suna fata wannan ziyarar ma zata kaiga kawowa kasar wani anfani na musamman.
Suna son Jamus ta kara taimakawa akan fannin noman rani domin kasar ta fita daga kuncin rayuwa da take ciki yanzu. Sun yi fatan dangantaka da suka fara yi da kasar Jamus shekaru 53 da suka gabata ta cigaba da karfafawa. Suna son a taimaka masu matasan Nijar su samu aikin yi domin su zauna cikin kasar maimakon yawon da su keyi a kasashen waje.
Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5