Taron, wanda da farko aka tsai da yau Talata don gudanar da shi, a maimakon haka sai ranar Jumma'a za a yi shi saboda dusar kankarar da ke fantsamowa a yankin tun daga daren jiya Litini.
Wani babban jami'in wannan gwamnatin ya ce ranar Jumma'a Trump "zai yi matukar sha'awar jin abin da Shugabar ta Jamus Merkel ta fahimta game da Putin yayin da ya ke gab da yin tozali da Shugaban na Rasha.
Masu suka daga bangarorin biyu sun yi ta nuna shakku game da abin da su ke ganin wauta ce Trump ke yi game da duk wani abin da ya shafi Putin, musamman game da yinkurin Rasha na yin katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka na 2016.
Wasu jami'an gwamnati hudu da su ka yi jawabi ga 'yan jarida gabanin ganawar da za a yi ran 17 ga watan nan na Maris, sun ce a ganinsu Shugaba Trump na so a mance da bambance-bambancen da ke tsakaninsa da Shugabar ta Jamus ne, wanda aka yi ta zance a kai.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5