A yau lahadi tsohuwar shugabar ta nufi gidanta dake Seoul inda daruruwan magoya bayanta ke zanga zangar tsigetan da akayi.
Kotun kundin tsarin mulkin ta gabatar da kuri’a a ranar Juma’a ta tsige Park, sakamakon rikicin da ya shafeta da kuma babbar kawarta.
Duk da haka ta zauna a Gidan gwamnatin mai suna Blue House a matsayin gidanta kafin ta koma gidanta na kanta wanda ya ka sance babu komai a cikinsa sai da aka sayi kayyakin da aka zuba a cikin gidan daga baya.
Dubunnan ‘yan kasar Koriya ta Kudu dake goyon bayan tsigeta ne suka bazama kan tituna a ranakun karshen makon nan suna d'aga tutoci gami da sowa, yayinda wasu kungiyoyin mutanen da suke goyon bayan Park suka ci alwashin bijirewa abinda suka kira “Kisan Gillar Siyasa.”
Jami’an ‘Yansanda a Seoul na zaton barkewar tashin hankali tsakanin bangarorin guda biyu musanman ma bayan kashe uku daga cikin masu gudanar da zanga zangar da akayi daga lokacin da aka sanar da tsige Park daga kan mulki.
Facebook Forum