Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Mota Ta Kutsa Cikin Mutane Ta Hallaka 34 a Haiti


A man looks at a bus that drove into a parade of pedestrians in Gonaives, Haiti, March 12, 2017.
A man looks at a bus that drove into a parade of pedestrians in Gonaives, Haiti, March 12, 2017.

A Haiti, akalla mutane 34 ne suka halaka, bayanda wata motar kiya-kiya wacce ta kade mutane take neman gudu ta fada cikin taron mutane jiya lahadi a birnin da ake kira Gonaives, kamar yadda jami'an kasar suka yi bayani.

Motar ta kade mutane biyu ta kashe daya dga cikinsu, matukin wanda ya nemi gudu daga wurin, ya afkawa wani taron mutane da suke sauraron wasu mawaka da suke nishadartar da su, ya kashe mutane 33. Wasu 17 kuma suka jikkata.

Birnin Gonaives, yana da tazarar kilomita 150 arewa da Port-au-prince, babban birnin kasar.

A halin da ake ciki kuma, adadin wadanda suka halaka atagwayen harin bama-bamai da aka kai akan wasu masallatan 'yan shi'a a birnin Damascuss na Syria ya kai 74, kamar yadda kungiyar kare 'yancin Bil'Adama ta Syria tayi bayani. Galibin wadanda harin ya rytsa da su 'yan kasar kasar Iraqi ne. Al'amarin ya auku ne jiya lahadi.

Wata kungiya mai alaka da al-Qaida ta dauki alhakin kai wannan hari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG