Debbie Wasserman Schultz, shugabar jam’iyyar Democrat ta ‘kasa, ta bar aikinta biyo bayan kwarmata wasu sakonnin email dake nuna shugabar na wasu kalaman cin zarafi ga mai neman zama ‘dan takara Sanata Bernie Sanders, a lokacin da yake karawa da Hillary don neman zama ‘dan takara. Wasserman Schultz, wadda take ‘yan majalisa ce da ta fito daga jihar Florida, ana tsammanin za ta sauka daga mukaminta karshen makon nan bayan babban taron da za ayi a birnin Philadelphia.
Bernie Sanders dai ya bukaci Wasserman Schultz da tayi murabus, bayan da aka kwarmata bayanan da suka kunshi email akalla 2000, na shugabar jam’iyyar na tsawon akalla shekara ‘daya da rabi.
Bayan da aka bayyana murabus ‘din Debbie, Bernie Sanders ya fitar da wata sanarwa dake cewa, “Debbie Wasserman Schultz, ta yanke shawara mai kyau ga jam’iyyar Democrat. Kuma ta cancanci a gode mata da shekarun da ta kwashe ta na aiki, yanzu jam’iyyar na bukatar sabon shugaba da zai bude kofar jam’iyyar yayi maraba ga ma’aikata da matasa. Dole ne shugabannin jam’iyyar su zamanto basa nuna banbanci ga kowa a zaben ‘dan takarar da za a tsayar.