WASHINGTON, D.C. - Shugabannin mulkin sojin sun rattaba hannu kan yarjejeniya mai taken Liptako-Gourma Charter, inda suka kafa kawancen kasashen Sahel. An kuma sanya wa yarjejeniyar sunan yankin da iyakokin kasashen uku suka hadu.
Kanal Assimi Goita, shugaban mulkin sojan Mali a cikin wata sanarwa ya ce "a yau na sanya hannu tare da shugabannin kasashen Burkina Faso da Nijar kan yarjejeniyar Liptako-Gourma, na kafa kawancen kasashen Sahel da nufin samar da tsarin tsaro na hadin gwiwa, da taimakon juna domin amfanin al'ummarmu."
Sabuwar yarjejeniyar ta yi kira ga kasashen uku da ke makwabtaka da juna da su yi kokarin kare juna. Dukkanin mutanen kasashen uku suna fuskantar barazana daga masu ikirarin jihadi. Kuma kowacce daga cikin kasashen an dai yi juyin mulki ne tun shekarar 2020.