Wasu daga cikin malaman da su ka jagoranci addu'oin sun ce sun fahimci matsalar tsaro ta sha karfin gwamnati ne shi ya sa suka koma ga mahalicci don neman mafita.
Dama dai ganin gazawar gwamnatin da wasu ke yi ya sa Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai jawo hankalin al'umma baki daya inda ya ke cewa mutane ba su ganin aikin da jami'an tsaro ke yi, suna kuma cikin zaginsu kuma hakan ba daidai ba ne saboda su ma ana kashe su a wurin yaki da ta'addanci.
Malam Samuel Aruwan shi ne kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, ya kara da cewa, gwamnati na iya bakin kokarinta don shawo kan matsallar tsaron.
A baya dai Giwa da Igabi ne kadai ke fama da matsalar tsaro a Lardin na Zazzau amma a 'yan kwanakin nan 'yan-bindiga sun matsawa hanyar Kaduna zuwa Zaria da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamallin da 'yan-bindiga suka shige ta har sau uku da kuma Zariar ma baki daya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5