Shugabannin Kungiyoyin Musulmi Sun Gudanar Da Wa'azin Zaman Lafiya

Shugabannin Kungiyoyin Musulmi A Taron Wa'azin Zaman Lafiya

Shugabannin addinin Islama daga kasashen Najeriya da Nijar sun gudanar da wa’azin kasa a karshen mako a birnin Yamai, inda suka maida hankali akan wasu mahimman ayyukan jin kai, yayin da malamai magada annabawan suka yi tunatarwa akan batutuwan da suka shafi zaman lafiya.

Shugabannin Kungiyoyin Musulmi A Taron Wa'azin Zaman Lafiya

Babban makasudun wannan haduwa ta wa'azin kasa a wannan jikon shine tunatar da jama’a muhimmancin zaman lafiya sakamakon lura da yadda kungiyoyin ta’addanci ke ci gaba da halaka rayukan bayin Allah da sunan jihadi a Yankin Sahel. Sheik Shitu Isa na daga cikin manyan wannan taro kuma ya jaddada batun zaman lafiya kamar yadda addinin Musulunci ke kiran a yi.

Najeriya da Nijar na daga cikin kasashen da suka fi dandana kudar wannan sabon al'amari, saboda haka malamai ke ganin bukatar hada kai domin karfafa ayyukan tunatarwa da fadakarwa kamar yadda Malam Muhamad Sani Ashir Kano ya ce.

Shugabannin Kungiyoyin Musulmi A Taron Wa'azin Zaman Lafiya

Gwamantin Nijar, a ta bakin Karamin Ministan Cikin Gida Mai Kula da Sha’anin Addinai Alkache Alhada, ya yaba da wannan yunkuri na shugabannin addinin Islama, domin a cewarsa ya zo akan dai dai idan aka yi la’akari da halin da ake cikiyau a kasashe 5 mambobin kungiyar G5 Sahel.

Saboda haka ya shawarcesu su matsa kaimi wajen jan hankulan jama’a akan batutuwan da ke da nasaba da halin da ake ciki a yau don samar da zaman lafiya a wannan yanki.

Shugabannin Kungiyoyin Musulmi A Taron Wa'azin Zaman Lafiya

Kungiyar Al Islam Kitab wa Sunnah mai masaukin baki, ta yi amfani da wannan dama don kaddamar da ayyukan wani sabon gidan marayu na hadin gwiwa da uwargidar Shugaban kasar Nijar Hajiya Aichatou Issouhou anan Yamai, da nufin daukar dawainiyar yara marayu. Sheik Chaibou Muhamad shi ne shugaban wannan kungiya.

Saurari rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabannin Kungiyoyin Musulmi Sun Gudanar Da Wa'azin Zaman Lafiya